Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-17 15:54:06    
An yi shawarwari tsakanin shugaban Sin Hu Jintao da firayin ministan kasar Mauritius

cri
A ran 17 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi shawarwari tare da firayin ministan kasar Mauritius Navinchandra Ramgoolam a Port Louis, inda suka tattauna kan dangantaka tsakanin Sin da Mauritius da sauran batutuwan da suka jawo hankulansu.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, shugabannin kasashen biyu za su halarci bikin sa hannu kan wasu takardu game da hadin gwiwa bayan da suka yi shawarwarin. Daga baya, Hu Jintao zai gana da shugaban kasar Mauritius.

A ran 16 ga wata, Hu Jintao ya isa Port Louis don fara ziyara a kasar Mauritius. Shugaba Hu ya yi wani jawabi, inda ya nuna imanin cewa, ziyarar za ta kara fahimta da amincewar juna, da karfafa dankon zumunci gami da inganta hadin gwiwa tsakaninsu don moriyar juna, ta yadda za a ciyar da dangantakar da ke tsakanin Sin da Mauritius zuwa gaba.

A cikin shekaru 37 da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Mauritius, dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu tana bunkasuwa lami lafiya. Musamman a cikin shekarun nan, ana yin mu'amala tsakaninsu, kuma an samu cigaba wajen hadin gwiwarsu a duk fannoni. Bangarorin biyu suna yin hadin gwiwa kan harkokin duniya da na yankuna.(Zainab)