Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-16 20:28:40    
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya isa kasar Mauritius

cri
A ran 16 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya isa Port Louis, babban birnin kasar Mauritius domin kaddamar da ziyararsa ta farko a kasar.

Firayim ministan kasar Mauritius Navinchandra Ramgoolam ya shirya gagarumin biki domin yin marhabin da zuwan shugaba Hu da 'yan rakiyarsa.

Shugaba Hu Jintao ya yi jawabi a filin jiragen sama, inda ya bayyana cewar bayan da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Mauritius, har kullum kasashen biyu su kan nuna girmamawa ga juna da yin zama daidai wa daida, da kuma hadin gwiwa sosai a fannonin tattalin arziki da cinikayya da al'adu da kuma aikin koyarwa. Ban da wannan kuma kasashen biyu su kan nuna goyon baya ga juna a cikin al'amuran duniya, don haka dangantakar da ke tsakanin Sin da Mauritius ta zama tamkar wani misali na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Shugaba Hu kuma ya yi imanin cewa, ziyarar za ta kara fahimta da amincewar juna, da karfafa dankon zumunci gami da inganta hadin gwiwa tsakaninsu don moriyar juna, ta yadda za a ciyar da dangantakar da ke tsakanin Sin da Mauritius zuwa gaba.(Kande Gao)