Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-16 15:39:10    
Za a yi hutu har kwanaki 7 don murnar sabuwar shekara ta al'umomin Tibet bisa kalandar gargajiya ta wurin

cri
Ranar 25 ga watan Febrairu na shekarar bana ita ce ranar sabuwar shekara ta al'umomin Tibet bisa kalandar gargajiya ta wurin, bisa labarin da ofishin kula da gwamnatin jama'ar birnin Lhasa ya bayar, an ce, za a yi hutu har kwanaki 7 don murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta al'umomin Tibet, watau za a yi hutu daga ranar 23 ga watan Febrairu zuwa ga ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2009.

Bisa labarin da aka samu daga hukumomin da abin ya shafa na jihar Tibet mai cin gashin kanta, an ce. Jihar Tibet da sauran wurare masu tafiyar da kalandar gargaiya ta Tibet za su huta kamar yadda ofishin kula da harkokin gwamnati ta birnin Lhasa ta tsara.

Bisa labarin da aka samu, an ce, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'a ta jihar ta tsara lokacin hutu kamar yadda aka samu a sauran wuraren kasar, kuma ta hada da lokacin hutu na sabuwar shekara ta al'umomin Tibet da bikin Shoton na al'umomin Tibet a cikin lokacin hutu na jihar tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta, watau an kara samun lokacin hutu na kwanaki 7 a gun bikin sabuwar shekara bisa kalandar al'umomin Tibet da bikin Shoton, kuma idan bikin sabuwar shekara ta al'umomin Tibet da bikin sabuwar shekara bisa kalandar al'umomin Han ba su hada kai tare ba, ma'aikata da manyan jami'an Tibet za su fi kara samun lokacin hutu na kwanaki 14 da ma'aikata na sauran jihohi a kasar Sin.(Bako)