Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-15 20:04:19    
Mutane daga sassa daban daban na zaman al'ummar kasar Mauritius suna zura ido kan ziyarar Hu Jintao

cri

Daga ran 16 zuwa ran 17 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao zai kai ziyara a kasar Mauritius wato wata kyakkyawar kasa tsibiri ce dake tekun India, wannan ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya ziyarci kasar Mauritius, haka kuma yana da muhimmiyar ma'ana. Mutane daga sassa daban daban na zaman al'ummar kasar Mauritius suna zura ido da kuma maraba da ziyarar Hu Jintao.

Shugaban kasar Mauritius Anerood Jugnauth ya furta a yayin da yake halartar liyafar bikin bazara da Sinawa mazauna kasashen waje suka kira cewa, ya gana da shugaba Hu Jintao a lokacin wasannin Olympic na Beijing na shekarar bara, inda suka sada zumunci a tsakaninsu sosai, yana maraba da ziyarar Hu Jintao don sake ganawa da shi.

Firaministan kasar Mauritius Navinchandra Ramgoolam ya nuna cewa, kasar Mauritius ta yi alfahari sosai don ziyarar da Hu Jintao zai kawo wa kasar, ziyarar Hu Jintao kuma ta zama wata kyakkyawar kyauta da zai bai wa jama'ar kasar Mauritius.(Lami)