Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-12 23:06:05    
Shugaba Hu Jintao ya sauka birnin Bamako na kasar Mali

cri
Ran 12 ga wata da yamma, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya sauka birnin Bamako, hedkwatar kasar Mali, inda ya fara ziyarar aikin a karo na farko a wannan kasa da ke yammacin Afirka.

A cikin jawabin da ya bayar a rubuce, shugaba Hu ya bayyana cewa, a cikin shekaru 49 da kasashen Sin da Mali suka kulla hulda a tsakaninsu, kasashen 2 sun yi ta raya zumunci a tsakaninsu, kana kuma sun sami sakamako da yawa sakamakon yin hadin gwiwa a fannoni daban daban. Kasar Sin na darajanta hulda a tsakaninta da kasar Mali, tana son gama kanta da Mali domin bude sabon shafi na yin hadin gwiwar abokantaka a tsakaninsu. Kazalika kuma, shugaba Hu ya nuna cewa, yana sa ran yin musayar ra'ayoyi tare da takwaransa na Mali Amadou Toumany Toure da sauran shugabannin Mali kan hulda a tsakanin kasashen 2 da al'amuran duniya da na shiyya-shiyya da ke jawo hankalinsu duka. Ya yi imani da cewa, a karkashin kokarin da bangarorin 2 suke yi, tabbas ne ziyararsa za ta iya inganta zumunci da hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 domin tinkarar kalubale tare da kuma samun bunkasuwa tare.

Shugaba Amadou Toumany Toure da wasu manyan jami'an gwamnatin Mali sun yi maraba da shugaba Hu da tawagar rakiyarsa a filin jirgin saman.(Tasallah)