Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-14 11:12:02    
Wu Bangguo ya gana da shugabannin kasar Seychelles

cri

A ran 13 ga wata, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mr. Wu Bangguo dake ziyarar sada zumunci a kasar Seychelles ya gana da shugaban kasar Mr. James Alix Michel, kuma ya yi tattaunawa da shugaban majalisar dokokin kasar Mr. Patrick Herminie.

Lokacin da ya gana da shugaban kasar Seychelles, Mr. Wu Bangguo ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Seychelles ta isa kyakkyawan misali ne ga manya da kanana kasashen suke zama tare bisa daidaici, da yin hadin gwiwa, da kuma taimakawa juna. Mr. Wu Bangguo ya gabatar da matakan da kasar Sin ta dauka don fuskantar matsalar kudin duniya, kuma ya bayyana cewa, bangaren kasar Sin zai ci gaba da samar wa bangaren kasar Seychelles taimako gwargwadon iyawarta.

Mr. Michel ya ce, bangaren kasar Seychelles ya nuna yabo da goyon baya ga kokarin da kasar Sin ke yi na kulla kyakkyawar dangantaka a tsakanin bangarorin biyu da kuma wasu fannonin harkokin yanki da na duniya. Ya nuna godiya ga bangaren Sin sabo da kulla hadin gwiwar abokantaka don moriyar juna da kasashen Afrika bisa tsarin dandanlin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika.

Lokacin da ya yi tattaunawa da Mr. Herminie, Mr. Wu Bangguo ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Seychelles tana cikin lokacin mafi kyau a tarihi. Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin tana son ta ci gaba da raya dangantaka dake tsakaninta da majalisar dokokin kasar Seychelles, shugabannin bangarorin biyu sun ci gaba da kai wa juna ziyara, a sa'I daya kuma, za a kara yin cudanya tsakanin kwamitin musamman da sauran hukumomi, da kuma yin musanyar sani game da raya kasa da raya dimokuradiyya da tsarin dokoki, don kara karfin bunkasuwar dangantakar dake tskanin kasashen biyu.

Mr. Herminie ya yaba da shawarar da Mr. Wu Bangguo ya yi kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da cudanya dake tsakanin majalisun biyu. (Zubairu)