Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-13 11:22:44    
An bude wurin shakatawa na tunawa da girgizar kasar da ta fadawa gundumar Wen Chuan a kasar Sin

cri
Bayan da girgizar kasa ta fadawa gundumar Wenchuan a kasar Sin, yanzu rabin shekara ke nan, a ranar 12 ga wata, an bude wurin shakatawa na tunawa da girgizar kasa da ta fadawa gundumar Wen Chuan a kasar Sin, watau wurin shakatawa da aka gina daura da harabar tarkacen gine-gine a Dong Hekou da ke gundumar Qingchuan a lardin Sichuan a kasar Sin.

Bisa labarin da muka samu, an ce, za a gina wurin bincike da tsarin yawon shakatawa da dakin baje-koli da dakunan nune-nunen aikin yaki da bala'in girgizar kasa da ceton mutane a wannan wurin shakatawa.

A ranar 12 ga wata, kungiyar ba da agaji ta Red cross masu aikin karfafa zukatan mutane, sun karfafa zukatan ma'aikata da suke aiki a wurin da bala'in girgizar kasa ya auku da kula da yara da suka samu raunuka a jikinsu da zukatansu. Zakarun gasar wasannin Olympic Deng Yaping da Gao Min da zakaran wasannin Olympic na nakasassu Sun Haitao sun je makarantar wurin don baiwa yara kwarin gwiwa.

A ranar 12 ga wata, wakilimmu ya sake ziyartar yankunan da bala'in girgizar kasa ya auku, kuma ya sami labari cewa, wadannan wurare na daukar matakai da dama don ba da tabbaci ga mutane da suke fama da bala'i don su samu wuraren kwana da tufafi da bargo maganin sanyi da abinci.(Bako)