Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-07 17:00:05    
Dalilai uku da suka haddasa rikicin kudi na duniya ba su yi babban tasiri ba ga gamayyar tattalin arziki na gabashin Asiya

cri

Ranar 6 ga wata, asusun ba da lamuni na duniya IMF ya bayyana cewa, dalilai uku da suka haddasa rikicin kudi na duniya ba su yi babban tasiri ba ga gamayyar tattalin arzki na gabashin Asiya wanda ya hada da Sin.

Bisa wani sabon rahoton hasashe da asusun IMF ya gabatar, an ce, dalilan da suka sa rikicin kudi na duniya bai kawo babban tasiri ga gamayyar tattalin arziki na gabashin Asiya ba, su ne, na farko, halin da hada-hadar kudi na wadanan kasashe ke ciki suna da kyau kwarai. Na biyu kuma shi ne, tattalin arziki na wadannan kasashe sun ci gajiya daga raguwar farashin manyan kayayyaki a kasashensu. Na uku kuma shi ne, gamayyar tattalin arziki na wadannan kasashe sun riga sun dauki matakai daga manyan fannoni wajen magance rikicin kudi na duniya.

Bisa wannan rahoto da aka bayar, an ce, makomar tattalin arziki na kasashen duniya ba ta yi kyau ba, kuma saurin karuwar tattalin arziki na shekarar bana da ta badi zai kai kashi 3.7cikin kashi 100, da kashi 2.2 cikin kashi 100. ko da yake saurin karuwar tattalin arziki na yankin Asiya da ya hada da Sin ya ja da baya, amma ya fi matsaikacin saurin karuwar tattalin arziki na dukkan duniya.(Bako)