Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-07 14:04:47    
Wu Bangguo ya isa birnin Libreville kuma ya fara yin ziyarar aikin a kasar Gabon

cri

Bisa gayyatar da Mr.Guy Nzouba Ndama shugaban majalisar dokoki na kasar Gabon ya yi, a ran 6 ga wata da yamma bisa agogon wurin, Shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo ya isa birnin Libreville, kuma ya fara yin ziyarar aikin ta kwanaki biyu a kasar Gabon.

A filin jiragen sama, Wu Bangguo ya gabatar da jawabi a rubuce, inda ya ce, tun daga kasashen Sin da Gabon suka kafa dangantakar diplomasiya a shekaru 34 da suka wuce, bisa kokarin da shugabannin da jama'ar kasashen biyu suka yi, dangantakar tsakaninsu ta samun bukasuwar sosai. Makasudin ziyararsa a kasar Gabon shi ne raya dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu kai sabon mataki.

A lokacin ziyararsa, Wu Bangguo zai gana da shugaban kasar Gabon Mr.Hadj Omar Bongo da shugaban majalisar dattawa Rene Radembino Coniquet da shugaban majalisar dokoki Guy Nzouba Ndama da sauran shugabannin bi da bi, kuma za su yi musanyar ra'ayoyinsu a kan dangantakar tsakanin kasashen biyu da batutuwan yankuna da na duniya da ke jawo hankulansu. Kuma bangarorin biyu za su kulla takadar hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikaya.(Abubakar)