Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-05 10:06:26    
Shugabannin kasar Algeria sun gana da Wu Bangguo kuma sun yi shawarwari da shi

cri

A ran 4 ga wata, Abdelaziz Bouteflika, shugaban kasar Algeria da Abdul-Aziz Ziari, shugaban majalisar dokoki ta kasar Algeria sun gana da Wu Bangguo, shugaban zaunanen kwamitin wajalisar wakilan jama'ar Sin a birnin Algiers, kuma sun yi shawarwari da shi.

Yayin da Bouteflika ya gana da Wu Bangguo, ya bayyana cewa, bangaren Algeria yana maraba da kamfanonin Sin da su zuba jari a kasar Algeria don kara hadin gwiwa tsakanin bangarori biyu a fannonin makamashi da ma'adinai da manyan ayyuka da sadarwa da dai sauransu.

Wu Bangguo ya ce, bangaren Sin yana fatan yin kokari tare da bangaren Algeria wajen fadada da zurfafa hadin gwiwar kamfanoni bisa ka'idar samun moriyar juna don samun bunkasuwar hadin gwiwar muhimman ayyukan da ke jagorantar duk fannoni kamar yankin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya.

A wannan rana, Wu Bangguo ya yi shawarwari da Ziari, shugaban majalisar dokoki ta kasar Algeria. Wu Bangguo yana fatan kasashen Sin da Algeria su kara hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a lokacin da ake cika shekaru 50 tun sa'ar da kasashen biyu suka kafa dangantakar diplomasiyya.

Ziari ya bayyana cewa, majalisar dokoki ta kasar Algeria tana son yin amfani da ayyukan hukumar tsara doka da fiffikonta na musanyar ra'ayoyin majalisun dokoki don kara yin shawarwari da inganta hadin gwiwar kasashen biyu a duk fannoni don sa sabbin abubuwa da sabon kuzari a cikin dangantakar tsakanin kasashen biyu.(Zainab)