Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-04 21:43:09    
Wu Bangguo ya isa birnin Algiers inda ya fara ziyarar aikinsa a kasar Algeria

cri

A ran 3 ga wata da yamma, Wu Bangguo, shugaban zaunanen kwamitin wakilan jama'ar kasar Sin ya isa birnin Algiers, inda ya fara ziyarar aiki ta sada zumunta a kasar Algeria.

Wu Bangguo ya bayar da wani jawabi a rubuce a filin jiragen sama, inda ya ce, yana farin ciki sosai da yin ziyarar sada zumunta a kasar Algeria a lokacin cikon shekaru 50 da aka kafa dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Algeria. A shekarar 2004, kasashen biyu sun kafa dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, kuma dangantakar a tsakanin kasashen biyu ta taka sabon mataki wajen bunkasuwa. Inganta da zurfafa zumuncin kasashen biyu ya dace da moriyar jama'arsu da fatansu, kuma ya amfanawa zaman lafiya da na karko da bunkasuwa na duniya. Ya yi imanin cewa, a karkashin kokarin bangarorin biyu, dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da aka kafa ta a tsakanin Sin da Algeria bisa zumuncin gargajiya za ta samu kyakkyawar makoma.(Zainab)