Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-04 21:08:27    
Mr. Hu Jintao zai halarci taron koli na shugabannin kasashen 20 game da kasuwar kudi da tattalin arzikin duniya

cri
A ran 4 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Mr. Qing Gang ya bayyana a gun taron manema labaru da aka shirya a nan birnin Beijing cewa, bisa gayyatar da shugaban kasar Amurka Mr. Bush ya yi, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao zai halarci taron koli na shugabannin kasashen 20 game da kasuwar kudi da tattalin arzikin duniya da za a shirya a ran 15 ga wata a birnin Washington.

Kazalika kuma, Mr. Qing Gang ya bayyana cewa, bisa gayyatar da shugaban kasar Peru Mr. Alan Garcia Perez ya yi, shugaba Hu Jintao zai halarci taron shugabannin kunigyar APEC a karo na 16 da za a shirya daga ran 22 zuwa ran 23 ga wata a birnin Lima, hedkwatar kasar Peru. Ban da wannan kuma, daga ran 16 zuwa ran 26 ga wata, shugaba Hu Jintao zai yi ziyarar aiki a kasashen 4, wato Costa Rica, da Cuba, da Peru, da Greece. (Zubairu)