Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-03 15:30:56    
Wu Bangguo ya tashi daga birnin Beijing zuwa kasashe 5 na Afirka don yin ziyarar aiki ta zumanta

cri
Bisa gayyata da shugabannin majalisun kasashen Algeria da Gabon da Ethiopia da Madagascar da Seychelles suka yi, a ran 3 ga wata da safe, shugaban zaunannen kwamitin majaliar wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo ya bar birnin Beijing cikin jirgin sama na musamman, don kai ziyarar aiki ta zumanta, kuma zai ziyararci kwamitin kungiyar AU da ke da cibiyarta a birnin Addis Ababa, babban birnin kasar Ethiopia.

Yayin da ya ke kan ziyarar, Wu Bangguo zai gana da shugabannin gwamnatocin da majalisun dokoki na kasashen da abin ya shafa kuma zai yi shawarwari tare da su, kuma zai yi musaya ra'ayoyi tare da su a fanonnin kara dangantakar tsakanin bangarorin biyu da kara hadin gwiwa tsakanin majalisun dokoki na bangarorin biyu, ban da haka kuma, Wu Bangguo zai halarci bikin sa hannu kan takardar hadin gwiwa kan tattalin arziki da fasahar tsakanin Sin da kasashen da abin ya shafa, da kuma yin binciken gana da halin tafiyar da ayyukan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Shugabannin zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da jami'in ma'aikatar harkokin wajen suna ganin cewa, zai kai ziyara a kasashen Afirka a shekarar da ake tabbatar da nasarorin da aka samu a wajen taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka, da kuma zai sa kaimi ga dangantakar aminci da hadin kai tsakanin Sin da kasashen 5 na Afirka, kuma sa kaimi ga zurfafa sabuwar dangantakar abokantaka bisa muhimman tsare-tsare tsakanin Sin da kasashen Afirka.(Abubakar)