Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-24 19:42:00    
Kasar Sin ta zama wata babbar kasa ce wajen samar da kayayyakin kananan sana'o'i a duniya

cri
Chen Shineng, shugaban kungiyar hadin gwiwa ta kananan sana'o'i ta kasar Sin ta yi bayani a kwanan nan, cewar kasar Sin ta riga ta zama wata babbar kasa ce da ta cancanci yin suna sosai a fannin samar da kayayyakin kananan sana'o'i a duk duniya, kuma tana kasancewa kamar cibiyar kera dimbin kayayyakin kananan sana'o'i ta kasa da kasa kana cibiyar sayen kayayyakin, ban da wannan kuma ta zama wani muhimmin wurin rarrabawa da kuma na samarwa a fannin cinikayya tsakanin kasa da kasa.

A cikin wadannan shekaru 30 da suka gabata bayan da kasar Sin ta bude kofa ga kasashen waje da kuma yin kwaskwarima a gida, halin da kananan sana'o'i na kasar Sin ke ciki ya samu kyautatuwa sosai. Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, yawan kudaden da kasar Sin ta samu daga wajen masana'antu na yin kananan sana'o'i na shekara ta 2007 ya zarce kudin Sin wato Yuan biliyan 7600, wanda ya ninka kusan sau 67 in an kwantanta da shekara ta 1978.(Kande Gao)