Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-10 15:15:27    
Ministan kula da harkokin matasa da wasannin motsa jiki na kasar Cape Verde ya yaba da ayyukan share fage da aka yi wajen shirya wasannin Olympic na nakasassu na Beijing

cri

A lokacin da yake ganawa da manema labaru na Gidan Radiyon Kasar Sin jiya, mataimakin firayim ministan kasar Cape Verde, kuma ministan kula da harkokin samari da wasannin motsa jiki na kasar Cape Verde, Mr. Sidonio Monteiro ya bayyana cewa, ayyukan share fagen wasannin Olympic na nakasassu na Beijing sun burge shi.

Mr. Sidonio Monteiro ya ce, wasannin Olympic na nakasassu na Beijing da ake yi sun bayyana yadda kasar Sin ta sauke nauyin dake wuyanta. Ya ce, "A ganina, an shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing da kyau. Mun gan yadda kasar Sin ta sauke nauyinta wajen shirya gasar wasannin Olympic, kuma kome na tafiya daidai yadda ya kamata. "

Mr. Sidonio Monteiro yana mai ra'ayi cewa, gasar wasannin Olympic da ta nakasassu ta inganta hadin gwiwa da zumuncin dake tsakanin jama'ar kasashen duniya. Ya ce, duk da kasancewar wasannin motsa jiki a kasar Cape Verde suna a baya, kasar Cape Verde ta aika da 'dan wasa daya kawai a gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, amma yana da muhimmiyar ma'ana ga kasar Cape Verde. Bugu da kari, ya ce, "Muna alfahari da ganin wani 'dan wasan kasar Cape Verde a filin gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. Wannan ya nuna cewa gwamnatin kasar Cape Verde ta mai da hankalinta da nuna babbar goyon baya ga wasannin Motsa jiki. "

A karshe dai, Mr. Sidonio Monteiro ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu nasarar shirya wasannin Olympic na yanayin zafi na shekarar 2008 na Beijing, ya yi imani da cewa, kasar Sin za ta samu nasarar yin wasannin Olympic na nakasassu na Beijing.(Asabe)