Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-10 15:14:15    
An shiga rana ta hudu da fara gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing

cri
Yau, an shiga rana ta hudu da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, za a bayar da lambabobin zinariya guda arba'in da shida a cikin gasannin tsalle-tsalle da guje-guje da iyo da dai sauransu.

A cikin gasanni na yau, za a bayar da lambobin zinariya guda 5 a cikin wasannin kwallon tebur tsakanin mace da mace. Zakarar wasannin Olympics na nakasassu a karo na biyar, wato 'yar wasan kasar Sin Zhang Xiaoling za ta shiga gasar kwallon tebur ta F8, za ta yi kokarin samun lambar zinariya ta shida. 'Yar wasan kasar Sin kuma zakarar wasannin Olympic ta Athens Liu Meili za ta shiga gasar kwallon tebur ta F9.

Kuma yau, 'dan wasan gasar sukuwar dawaki na farko na kasar Sin Peng Yulian zai shiga gasar sukuwar dawaki ta gasar wasannin Olympic ta nakasassu da aka yi a filin sukuwar dawaki na Shatian a birnin Hongkong, wannan ne karo na farko da 'dan wasan gasar sukuwar dawaki na babban yankin kasar Sin ya shiga gasannin wasa sukuwar dawaki na wasannin Olympic na nakasassu.

Bugu da kari, za a bayar da lambobin zinariya guda hudu a cikin wasannin daukan nauyi. 'Dan wasa mai shekaru 46 Wu Guojing zai shiga gasar daukar nauyi ta ajin kilo 52 ta maza, kuma 'yar wasa da ba ta kai shekaru 20 ba Shi Shanshan za ta shiga gasar daukar nauyi ta ajin kilo 48 ta mata.

Dadin dadawa, za a bayar da lambobin zinariya guda sha biyu a cikin wasannin iyo. Mai daukar tutar kungiyar wakilan kasar Sin Wang Xiaofu, da 'dan wasa da ya sami lambobin zinariya guda hudu a wasannin Olympic na Athens He Junquan za su shiga iyon rigingine da gasar iyo na yada kanin wani na tsawon mita dari-dari na hudu-hudu.(Asabe)