Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-09 11:23:01    
Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun yaba wa bikin bude gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing

cri

Bayan da bude gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing a daren ran 6 ga wata, kafofin watsa labaru na kasashen Singapore da Malasiya da Panama da Cuba da Indunisiya sun bayar da sharhi cewa, bikin bude gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing ya bayyana halayen nakasassu na yin kwazo da himma da samar da abin al'ajabi.

Jaridar Lianhe Zaobao ta Singapore ta bayar da wani labari a ran 8 ga wata cewa, wasannin Olympics na Beijing ya bayyana karfin gwamnatin Sin, kuma ya shaida wa duniya bunkasuwar zamantakewar al'ummar kasar Sin. Bikin bude gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing ya cika da tunanin jin kai na dan Adam. Labarin ya ce, nasarar da wasannin Olympics na Beijing ya samu ta bayyana karfin gwamnatin Sin, kuma ta shaida wa duniya bunkasuwar zamantakewar al'ummar kasar Sin.

Kafofin watsa labaru na Malasiya sun bayyana a ran 8 ga wata cewa, bikin bude gasar ya bayyana ma'anar rai, kuma ya burge jama'a sosai. Gasar wasannin Olympics ta nakasassu tana da kyau kamar gasar wasannin Olympics, ta haka an gano kasar Sin ta dora muhimmanci a kan gasar wasannin Olympics ta nakasassu.

Jaridar International Daily News ta Indunisiya ta bayar da wani sharhi cewa, wasannin Olympics na nakasassu na Beijing ya bayyana halayen nakasassu na nuna kwazo da himma da son rai da samar da abin al'ajabi kamar sauran mutane, kuma za su ba da gudummowa a kan bunkasuwar al'adun dan Adam. Wasannin Olympics na nakasassu na Beijing ya bayyana jin kai da hakuri na al'adun gargajiya na Sin.(Zainab)