Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-08 11:23:49    
Mr Sagarra ya yaba wa bikin bude gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing

cri

A ran 7 ga wata da dare, yayin da Miguel Sagarra, mataimakin shugaban kwamitin wasannin Olympics na nakasassu na duniya ya ke hira da wakilin gidan rediyon kasar Sin, ya bayyana cewa, bikin bude wasannin Olympics na nakasassu na Beijing yana da kyau sosai, kuma ya burge jama'a ta yadda ba za su mantawa da ba bikin har abada.

Mr Miguel ya halarci walimar maraba da zuwan 'yan wasan nakasassu na Portugal da aka yi a gidan jakadanci na Portugal bisa gayyata. A gun walimar, Mr Miguel ya bayyana cewa, bikin bude wasannin Olympics na nakasassu na Beijing da aka yi a daren ran 6 ga wata ya sanya masa kyakkyawar alama, bikin yana da kyau kuma da karfin mamaki sosai, kuma ya burge kowane mutum sosai.

Mr Miguel ya ce, wasannin Olympics na nakasassu na Beijing shi ne kasaitaccen taron da dukan 'yan wasan nakasassu suke taruwa gu daya, kuma su iya shaida kansu a gasannin.(Zainab)