Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-04 19:27:23    
Girgizar kasa da ta auku a Wenchuan ya yi sanadiyar asarar kudin Sin yuan biliyan 845.1 kai tsaye

cri
Ran 4 ga wata, Shi Peijun, mataimakin darektan kwamitin kwararru masu nazarin girgizar kasa da ta auku a Wenchuan na kasar Sin ya bayyana cewa, girgizar kasa da ta auku a Wenchuan ta riga ta yi sanadiyar asarar kudin Sin yuan biliyan 845.1 kai tsaye a lardunan Sichuan da Gansu da Shaanxi, kuma yawan asarar da Sichuan ta samu ya kai kashi 91 cikin dari bisa jimlar asarar.

A gun taron manema labaru da ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya, Mr. Shi ya ce, a cikin asarar da aka samu a sakamakon girgizar kasa ta Wenchuan, yawan asarar da aka samu daga wajen lalacewar gidaje ya wuce kashi 27 cikin dari, yawan asarar da aka samu daga wajen lalacewar makarantu da asibitoci da sauran gine-ginen ba na gidaje ba ya wuce kashi 20 cikin dari.

Wata sabuwa kuma, yanzu an kammala galibin aikin kimantawa da aka yi wa wuraren da girgizar kasa ta Wenchuan ta shafa game da asarar da suka yi. A cikin lardin Sichuan, yawan wuraren da suka sha wahala mafi tsanani da kuma wadanda suka sha wahala ya kai 39, haka kuma, a lardin Gansu, akwai irin wadannan wurare 8, a lardin Shaanxi kuwa, akwai wasu 4. Ban da wannan kuma, fadin wadannan wurare 51 ya wuce murabba'in kilomita dubu 130.(Tasallah)