Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-03 21:52:35    
Kasar Sin ta samu cigaba kan aikin kiyaye nakasassu a shekara ta 2007

cri
A ran 3 ga wata, tashar internet ta gwamnatin kasar Sin ta yi amfani da abubuwa na "Sanarwar kididdiga game da bunkasuwar da kasar Sin ta samu a fannin aikin kiyaye nakasassu a shekara ta 2007" da hadaddiyar kungiyar nakasassu ta kasar Sin ta bayar, inda aka nuna cewa, "shekara ta 2007 shekara ce da aka samu sabbin kyawawan cigaba cikin sauri a kan harkokin nakasassu".

Bisa wannan sanarwa, an ce, a shekara ta 2007, an warkar da nakasassu fiye da miliyan 5 da dubu dari 3 bayan da kasar Sin ta samar da wasu muhimman ayyukan warkar da nakasassu.

A waje daya kuma, a shekara ta 2007, an tabbatar da ikon samun ilmi na nakasassu. Yawan nakasassun da suke karatu a makarantu iri daban daban ya kai dubu 580.

Sannan kuma, wannan sanarwa ta bayyana cewa, a shekara ta 2007, yawan nakasassun da suka samu aikin yi a birane da garuruwa ya kai dubu 390 tare da nakasassu miliyan 17 da suke zama a kauyuka suka samu aikin yi.

Haka kuma, a shekara ta 2007, an samu kyautatuwa wajen ba da tabbaci ga zaman rayuwar nakasassu. An kuma samu ci gaba wajen taimakawa nakasassu wajen fama da talauci. Sakamakon haka, a bayyane ne zaman rayuwar nakasassu ya samu kyautatuwa.

Kazalika, a shekara ta 2007, kasar Sin ta shirya gasar Olympic ta musamman ta duniya ta karo na 12 cikin nasara, an kuma kara mai da hankali kan share fagen gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing ta shekara ta 2008. (Sanusi Chen)