Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-14 16:29:56    
Za a mai da kiyaye zaman rayuwar jama'a ya zama tushen farfado da sake gina yankin da ta yi fama da girgizar kasa na gundumar Wen Chuan

cri
A ran 14 ga wata, wani jami'in kwamintin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya bayyana cewa, za a mai da kiyaye zaman rayuwar jama'a ya zama tushen farfado da yankin da ta yi fama da girgizar kasa na gundumar Wen Chuan.

A lokacin da jami'in nan ya gana da manema labaru a kan babban shirin sake gina yankin Wen Chuan, ya bayyana cewa, burin sake gina yankin nan shi ne, kowane iyali yana da gidan zama, da kowane iyali yana da aikin yi, da kowane mutum ya samu kariya, ban da wannan kuma za a inganta manyan ayyuka, da bunkasa tattalin arziki, da kuma kyautata muhalli. A bisa ka'idar nan, za a ci gaba da kokari, sabo da haka, mutane dake cikin yankin girgizar kasa za su shiga zama mai wadata tare da duk jama'ar kasar Sin.

Bisa shirin nan, kasar Sin za ta yi shekaru 3 ta yi amfani da RMB biliyan dubu daya don sake gina yankin nan.(Asabe)