Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar an ce, ana bukatar kimanin kudin Sin Yuan biliyan dubu goma wajen sake gina gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan bayan bala'in girgizar kasa.
" Babban shirin farfado da yankin Wenchuan bayan bala'in girgizar kasa" ya tanadi cewa, lardin Sichuan, da lardin Gansu da kuma lardin Shanxi su ne suka fi fama da bala'in girgizar kasa, wanda ya kuma rutsa da mutane kimanin miliyan 19 da dubu 867.
An labarta cewa, tun daga ranar yau zuwa ranar 24 ga wata, an soma jin ra'ayoyin jama'a kan wannan babban shiri. ( Sani Wang )
|