Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-12 20:45:19    
Dukkan masu fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan, wadanda yawansu ya wuce miliyan 10 sun samo gidajen kwana na wucin gadi

cri
A ranar 12 ga wata, gwamnatin lardin Sichuan ta sanar da cewa, masu fama da bala'in girgizar kasa na lardin sama da miliyan 10, wadanda suka rasa gidajensu, ko gidajensu suka lalace, sun riga sun samu gidajen kwana na wucin gadi. Ya zuwa yanzu, an riga an kawo karshen ayyukan sake tsugunar da masu fama da bala'in a dukkan fannoni.

Ranar 12 ga watan Agusta, ranar cikon watanni 3 ce da aukuwar babbar girgizar kasa da karfinta ya kai awo 8 bisa ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan. Kasar Sin ta warware matsalar gidajen kwana ta mutane masu fama da bala'in fiye da miliyan 10 cikin kusan watanni 3 kawai. (Bilkisu)