Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-12 16:12:53    
Zaman rayuwar mutane masu fama da bala'in girgizar kasa fiye da miliyan 15 ya samu tabbatatuwa

cri
A kwanan baya, hukumar fama da bala'i daga indallahi da ba da kayayyakin jin kai ta ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta bayar da labari cewa, bayan watanni 3 da aka samu bala'in girgizar kasa a wasu wuraren kasar Sin, an riga an tabbatar da kusan dukkan mutanen da suke zama a yankunan fama da bala'in da suna samun abinci da tufafi da ruwan sha mai tsabta da wuraren kwana.

An labarta cewa, gidaje da yawa sun ruguje sakamakon bala'in girgizar kasa, yawan mutanen da suka bar yankuna masu fama da bala'in ya kai fiye da miliyan 15 da dubu dari 1. Wani jami'in ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar Sin ta riga ta kebe wa yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa na Wenchuan kudin agaji da yawansa ya kai fiye da kudin Renminbi yuan biliyan 38 tare da tantuna kusan miliyan 1 da dubu 580. A waje daya kuma, an sama wa mutane masu fama da bala'in wasu kudin yau da kullum da abinci da kudin tallafi domin gina gidaje. (Sanusi Chen)