Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-08-11 21:34:38    
Aikin yaki da bala'in girgizar kasa da ceto a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin

cri

Ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar da wani labari bisa ikonsa daga babban ofishin ba da jagoranci wajen yaki da bala'in girgizar kasa da ceto ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin cewa, ya zuwa karfe 12 na ranar 11 ga wata, an tabbatar da cewa, mutane dubu 69 da dari 2 da 25 sun mutu, a yayin da mutane dubu 17 da dari 9 da 39 suka bace a sakamakon girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin.

Gwamnatoci daban daban na kasar Sin sun bayar da kudin Sin Yuan biliyan 64.4, al'umomi daban daban na kasar Sin sun bayar da kudin kyauta da yawansu ya kai kudin Sin Yuan biliyan 59.2, an riga an bayar da biliyan 23.8 daga cikinsu ga yankunan girgizar kasa.(Danladi)