Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-25 21:47:58    
Kasar Sin za ta kawo karshen gina dakin ajiye kayayyakin girgizar kasa ta na '5.12' a cikin shekaru 2 ko uku masu zuwa

cri

Mataimakin darektan kula da gidajen ajiye kayyyakin tarihi na hukumar tsofaffin abubuwab al'adu ta kasar Sin Mr. Li Yaoshen ya bayyana a ran 25 ga wata a birnin Beijing cewa, cikin shekaru 2 zuwa 3 masu zuwa, kasar Sin za ta kawo karshen gina dakin ajiye kayayyakin tarihi game da bala'in girgizar kasa da ya faru a gundumar Wenchuan a ranar 12 ga watan Mayu wato '5.12'.

Mr. Li ya bayyana a gun wani taron manema labaru da aka shirya a ran nan cewa, gwamnatin lardin Sichuan ta riga ta gabatar da shirin kafa gidan ajiye kayayyakin ga kungiyar da ke kula da harkokin sake raya yankuna masu fama da bala'in bayan bala'u ta kasar Sin a ran 18 ga wata. Bisa abubuwan da aka tanada a cikin shirin, an ce, babban aiki na dakin ajiye kayayyakin bala'in girgizar kasa zai bayar da taimako a fannoni da dama, wadanda suka hada da bayyana tarihi, da nuna ta'aziyya ga wadannan suka mutu, da yin gargadi, da ba da ilmi, da yin nazari da dai sauransu.(Danladi)