Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-19 20:20:05    
Kasuwannin yawon shakatawa na lardin Sichuan sun fara farfadowa

cri
Kwanan baya a nan binrin Beijing, an gudanar da taron sa kaimi ga harkokin yawon shakatawa na lardin Sichuan. Wani jami'in sassan da abin ya shafa na lardin Sichuan ya ce, kasuwannin yawon shakatawa na lardin Sichuan sun fara farfadowa.

An ce, fadin yankunan da girgizar kasa ta shafa a lardin Sichuan bai kai kashi 20% na dukan fadin lardin ba, kuma akasarin wuraren yawon shakatawa a lardin ba su lalace ba. Ya zuwa yanzu, lardin Sichuan ya riga ya farfado da kasuwannin yawon shakatawa a duk fadin birane 13 na lardin, tare kuma da wasu wuraren shakatawa a birane 6.

Masanan ilmin girgizar kasa sun bayyana cewa, ba safai a kan samu girgizar kasa da karfinta ya kai digiri 8 ba ko a cikin dubban shekaru, bayan aukuwar girgizar kasa a gundumar Wenchuan, a cikin wani lokaci mai tsawon gaske ne za a sake tara karfi mai yawan haka. Sabili da haka, aukuwar girgizar kasa a gundumar Wenchuan na nufin kara samun tsaro a maimakon hadari a shiyyar da ta kewayenta.(Lubabatu)