Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-18 22:10:42    
Ba a sami yaduwar cututtuka masu tsanani ba a yankunan da girgizar kasa ta shafa

cri
Yau 18 ga wata a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin, Mr.Mao Qun'an ya bayyana cewa, ba a sami yaduwar cututtuka masu tsanani ba a yankunan da girgizar kasa ta shafa a nan kasar Sin.

A gun taron manema labarai, Mr.Mao Qun'an ya ce, bisa ga nazarin da aka yi kan yankunan da girgizar kasa ta shafa, an ce, yawan kamuwa da cututtuka masu yaduwa a yankunan ya ragu idan an kwatanta shi da na makamancin lokacin shekarar bara, ba a sami yaduwar cututtuka masu tsanani ba, kuma ana warkar da wadanda suka raunata kamar yadda ya kamata.

Ya kara da cewa, yanzu an farfado da yawancin tashoshin sa ido kan cututtuka masu yaduwa a yankunan da girgizar kasa ta shafa, kuma ana iya sa ido a kan cututtuka masu yaduwa da kuma ba da rahotanninsu cikin lokaci.(Lubabatu)