Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka Tana Kare Hakkin Dan Adam Ko Kuma Keta Shi?
2020-11-11 20:27:10        cri

 

 

A wajen taron kwamitin hakkin dan Adam na MDD da ya gudana a kwanakin baya, an tantance batun hakkin dan Adam a kasar Amurka, inda kasashe fiye da 110, ciki har da kawayen kasar Amurka, suka shiga jerin masu nuna shakku kan batun kare hakkin dan Adam a kasar daya bayan daya. A daidai lokacin da ake gudanar da taron, yawan Amurkawa da suka kamu da cutar COVID-19 ya zarce miliyan 10, kana wadanda suka cutar ta halaka sun kusan kai dubu 240.

Yadda ake samun yaduwar cutar COVID-19 sosai a kasar Amurka, da yadda kasashe daban daban ke sukarta, sun nuna lalacewar yanayin hakkin dan Adam na kasar. Ko da yake 'yan siyasan kasar Amurka su kan soki batun kare hakki dan Adam na sauran kasashe, amma a wannan karo su da kansu ba za su iya amsa wannan tambaya ba, wato, me ya sa kasar Amurka, a matsayinta na kasa mafi karfin tattalin arizki da kimiyya da fasaha, musamman ma a bangaren fasahohin aikin jinya, take samun mafi yawan masu kamuwa da cutar COVID-19, da wadanda suka rasa rayukansu sakamakon cutar a duniya? Hakkin rayuwa na daga cikin muhimmin hakkin dan Adam. Sai dai yanzu haka ana kokarin keta wannan hakki a kasar ta Amurka.

Kuma dalilin da ya sa haka, shi ne domin 'yan siyasan kasar sun fi mayar da hankali kan batun da ya shafi siyasa, da moriyar masu hannu da shuni, maimakon rayukan jama'a. Sun yi biris da gargadin da masana kimiyya suka yi, da kokarin siyasantar da cutar COVID-19, da neman kare tattalin arziki ba tare da martaba matakan kandagarki ba.

Ban da keta hakkin dan Adam a cikin gida, kasar Amurka na kokarin ta da matsala a sauran kasashe. Misali, takunkumin da ta kakabawa kasar Iran, ya sa jama'ar kasar shiga cikin kuncin rayuwa, musamman ma a lokacin da kasar ke fama da cutar COVID-19. Sai dai maimakon kai dauki ga Iran, kasar Amurka ta tsaurara mata matakan takunkumi.

Tuni al'ummar duniya ta gano manufar Amurka, na fakewa da batun kare hakkin dan Adam, domin kokarin keta shi. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China