Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guntun Gatarinka Ya fi Sari ka Ba ni
2020-11-11 17:26:55        cri

Kowace kasa a duniya tana da wasu albarkatu da Allah ya hore mata, wanda idan ta yi amfani da su yadda ya kamata, zai taimaka mata wajen biyan bukatunta ko cimma wani buri da take fatan aiwatarwa, har ma ta inganta rayuwar al'ummarta. Sai dai duk da tarin albarkatun makamashin da ake iya sabuntawa dake jibge a nahiyar, yanzu haka akwai kusan, sama da mutane miliyan 600 dake zaune a sassa daban-daban na nahiyar da ba sa iya samun hasken wutar lantarki.

Wannan ya sa aka kira wani taron samar da wutar lantarki bisa tururin karkashin kasa (ARGeo-C8), taron da ya hallara masana daga sassan samar da wutar lantarki bisa karfin tururin karkashin kasa, da tsoffin shugabannin kasashe da mambobin kungiyar samar da makamashi bisa karfin tururi daga sassan Afirka, da Turai da Asiya, a wani mataki na samar da kimanin MW 20,000 na makamashi bisa tururi a Afirka.

Manufar taron ita ce bunkasa fasahar samar da makamashi bisa karfin tururin karkashin kasa a yankin gabashin Afirka.

Masu fashin baki na cewa, ya dace kasashen nahiyar, su yi amfani da albarkatun da Allah ya ba su, da ma kudaden shigar da ake samu daga albarkatun karkashin kasa, domin biyan bukatunsu su kuma tunkari matsalar tattalin arziki dake alaka da annobar COVID-19, kuma hakan zai taimaka wajen cike gibin kasafin kudi a nahiyar yayin da ake fama da wannan annoba da ma bayan ta.

Sanin kowa ne cewa, duk da irin wadannan albarkatu dake makare a karkashin kasa a sassan nahiyar wadanda ka iya zama mafita, raguwar ci gaban tattalin arziki saboda annobar gami da wasu matsaloli da suka dabaibaye nahiyar, na iya tarnaki ga samar da muhimman hidimomi da gwamnatocin nahiyar suka tsara aiwatarwa a bangarorin lafiya da na ilimi da tsaftaccen ruwan sha da sauran muhimman fannoni na rayuwa.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, kiddidigar bankin raya nahiyar AFDB, ta nuna cewa, talauci ya karu a nahiyar saboda kalubalen da annobar ta haifar.

Haka kuma annobar COVID-19 ka iya jefa karin mutane miliyan 28.2 zuwa miliyan 49.2 na nahiyar cikin matsanancin talauci, wanda kuma zai kawo cikas ga kokarinsu na ba da gudunmawa ga ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063. Koma dai mene ne, kamata ya yi kasashen nahiyar su zage damtse, wajen sarrafa albarkatun da suke da su, don tsira da mutuncinsu da na jama'arsu. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China