Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shawarwarin gina makomar bai daya ta fannoni hudu sun nuna hanyar raya kungiyar SCO
2020-11-11 16:55:30        cri

Wata hadaddiyar sanarwa, da sanarwoyin hadin gwiwa guda shida, da kuma yarjejeniyoyin hadin gwiwa a fannoni daban daban sun shaida nasarorin da aka samu a gun taron kolin shekara-shekara na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO da aka gudanar ta yanar gizo. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bada muhimmin jawabi a gun taron kolin a ranar jiya, inda ya nanata tunanin Shanghai, da kuma bada shawarwarin gina makomar bai daya a fannoni hudu karkashin tsarin kungiyar, wadanda suka nuna hanyar raya kungiyar SCO, kana aka inganta tsarin neman makoma ta bai daya ta dukkanin dan Adam, wanda hakan ke da babbar ma'ana ga tabbatar da zaman lafiya da samun bunkasuwa a duniya.

Bisa yanayin tinkarar cutar COVID-19 da manyen sauye-sauyen da ke faruwa a duniya, kasa da kasa sun jaddada tunanin Shanghai wato yin imani da juna, da samun moriyar juna, da nuna daidaici, da yin shawarwari, da girmama juna, da kuma neman samun ci gaba tare, kana a karo na farko ne shugaban kasar Sin ya gabatar da shawarwarin gina makomar bai daya a fannoni hudu karo a karkashin tsarin kungiyar, wato a fannonin kiwon lafiya, da kiyaye tsaro, da samun bunkasuwa, da kuma raya al'adu, wadanda suka samar da dabarun Sin na warware matsalolin da ake fuskanta duniya.

Ban da wannan kuma, Sin ta nuna goyon baya ga hukumar kiwon lafiya ta duniya wajen taka rawa mai jagoranci, da kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa, da yin la'akari da bukatun kasashe membobin kungiyar SCO kan allurar rigakafin cutar COVID-19, da shigar da su bikin baje kolin CIIE, hakan ya kara samar da imani da karfi ga kasashe membobin kungiyar SCO, wajen yaki da cutar COVID-19 da zurfafa hadin gwiwarsu a dukkan fannoni. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China