Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta sha alwashin kara hade sassan kungiyar hadin kai ta Shanghai
2020-11-11 16:06:46        cri
Mataimakin ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Le Yucheng, ya ce a matsayin ta na daya daga cikin kasashen da suka kafa kungiyar hadin kai ta Shanghai ko SCO a takaice, kasar Sin ta kuduri aniyar yin aiki tare da sauran kasashe mambobin kungiyar, ta yadda za a kai ga nasarar kusantar juna, da kafa al'umma mai makomar bai daya tsakanin mambobin ta.

Mr. Le ya bayyana hakan ne a nan birnin Beijing, bayan kammala taro na 20, na majalissar shugabannin kasashe mambobin kungiyar ta SCO. Ya ce yanayin da ake fuskanta a matakai na kasa da kasa, da na shiyya shiyya, na sauyawa cikin yanayi mai sarkakiya, don haka SCO na fuskantar sabbin damammaki, da kalubale na ci gaban ta.

Kaza lika karkashin wannan yanayi, kungiyar SCO ta yi nasarar gudanar da taronta ta kafar bidiyo, tare da cimma sakamako mai gamsarwa, wanda ke da muhimmanci da tarin alfanu ga mambobin ta.

Har ila yau, taron na SCO ya dada karfafa karfin gwiwa, da jajircewar dukkanin sassa a fannin yaki da annobar COVID-19, ya kuma fayyace inda aka sa gaba game da manufofin kungiyar, tare da tabbatar da muhimman kudurorin zurfafa hadin gwiwar ta. Bugu da kari taron ya kara tabbatar da matsayar sassan kasa da kasa, game da bukatar ci gaba da cudanyar dukkanin sassa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China