Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Darajar yarjejeniyoyin da aka kulla a yayin CIIE ta zarce dalar Amurka biliyan 72
2020-11-11 14:17:59        cri

A jiya Talata 10 ga watan nan ne aka rufe bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasar Sin (CIIE) karo na 3 a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin. Duk da annobar COVID-19 dake ci gaba da addabar wasu sassan duniya, an nuna matakar sha'awa kan yin hadin gwiwa a yayin bikin. An kulla yarjejeniyoyi a fannin sayen kayayyaki da hidimomi na shekara guda da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 72.62, karuwar kaso 2.1 cikin 100 kan na bikin shekarar da ta gabata. Baya ga haka, daruruwan kamfanoni sun yi rajista da kulla yarjejeniyoyi na halartar bikin karo na 4.

Yayin da aka gudanar da bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasar Sin karo na 3, wasu kamfanoni sun yaba wa rawar da bikin yake takawa, sun kuma nuna fatan alheri kan bikin karo na 4.

A yayin taron dandalin tattaunawa mai taken "zuba jari ta hanyar ba da tasiri, a kokarin sake gina kyakkyawar duniya" a lokacin gudanar da bikin na CIIE, Madam Anna Pawlak-Kuliga, shugabar kamfanin IKEA a kasar Sin, kuma babbar darekta mai kula da ayyukan ci gaba mai dorewa, ta gaya wa manema labaru cewa, "Tabbas kamfaninmu na IKEA zai halarci bikin CIIE karo na 4. A gani na, bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasar Sin, wani dandali ne mai matukar kyau, inda ake mu'amala da cudanya da masu sayayya da takwarorin su, ana musayar ra'ayoyi masu ban sha'awa, kana kuma, ana samun damar kara sanin yadda sauran kamfanoni suke tafiyar da harkokinsu. Har ila yau kuma, a yayin irin wannan dandali, an samu damar yin tattaunawa kan wasu batutuwa yadda ya kamata. Har ma an kai ga samun damar cudanya da unguwannin wurin, da kuma kananan hukumomin wurin. Lamarin da ya samar mana yanayi mai kyau, wajen habaka kasuwa da kuma kyautata ciniki."

Kamfanin Vorwerk na kasar Jamus ya halarci bikin a shekaru uku a jere. Babban darektan kamfani mai kula da harkokin nahiyar Asiya da tekun Fasific Fredrik Lundqvist ya zanta da wakilinmu, inda ya nuna cewa, kamfaninsa ya cika alkawarin da ya yi a shekarar 2019 da ta gabata, wato fadada fadin wurin nune-nunen kayayyaki a yayin bikin na CIIE a karo na 3 da kusan kashi 40 cikin kashi dari bisa na shekarar 2019. Sa'an nan kuma, a watan Yulin bana, wannan kamfanin Jamus ya zama daya daga cikin kamfanoni na rukuni na farko, da suka kulla yarjejeniyar halartar bikin na CIIE daga shekarar 2020 zuwa 2022. Mista Lundqvist ya ce, "Kamfaninmu na sha'awar bikin CIIE. Muna farin ciki da ganin cinikinmu yana karuwa a ko wace shekara. Don haka za mu ci gaba da kokarinmu bisa wannan manufa. Mun kulla yarjejeniya ta halartar bikin a shekara mai zuwa. Za mu ci gaba da fadada wurin nune-nunenmu a shekara mai zuwa, da zummar kara samun sakamako mai kyau."

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China