Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masani: Wajibi ne kasashen yammacin duniya su kauracewa haifar da matsala ga aikin gina kasashen Afirka bayan yaduwar cutar COVID-19
2020-11-11 11:20:46        cri

A ranar 9 ga wannan wata na Nuwamba, jaridar The Nation da ake wallafawa a tarayyar Najeriya, ta gabatar da wani bayani mai taken "matsalolin da ake fama da su yayin da ake sake daidaita basussuka, da rikicin ciniki, da tashe-tashen hankula a duniya".

Jawabin, wanda jagoran kungiyar samar da jin kai ga wadanda suka rasa gidajen su a kasar Samuel Akpkbome Orovwuje ya rubuta, ya nuna yabo ga kasar Sin, bisa cika alkawarin da ta yi na rage basussukan da ta baiwa kasashe da dama, da kuma kokarin samun moriyar juna a yayin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, kana ya sossoki kasashen yammacin duniya ciki har da Amurka, da su yi amfani da tsarin hada-hadar kudi na duniya, don haifar da matsala ga aikin gina kasashe masu tasowa bayan yaduwar cutar COVID-19.

Sharhin ya bayyana cewa, kasashen yammacin duniya kamar kasar Amurka, na sarrafa akalar tsarin hada-hadar kudi na duniya, wanda hakan ke tsananta yanayin raguwar tattalin arzikin kasashen Afirka, kuma aikin nasu na yin kama-karya ya haifar da rashin adalci ga tsarin hada-hadar kudi na duniya a dogon lokaci.

Ya ce Sin kasa ce da ke kyautata tattalin arzikin duniya, idan aka kwatanta ta da Amurka, wadda ke son aiwatar da ikon kama karya. Kaza lika mu'amalar samun moriyar juna dake tsakanin Sin da Afirka, ita ce dangantakar hadin gwiwar samun moriyar juna. Don haka tilas ne kasar Amurka ta dakatar da hana bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, don maida hadin gwiwarsu kara amfanawa kasashen Afirka. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China