Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a bude baje kolin fasahohin zamani a birnin Shenzhen
2020-11-11 10:23:57        cri

Daga yau Laraba har zuwa Lahadi ne, 'yan kasuwa da masu zuba jari daga kasashen duniya da ma wasu kungiyoyin kasa da kasa sama da 50, za su halarci bikin baje kolin fasahohin zamani na kasar Sin karo na 22.

Baje kolin na CHTF zai gudana ne a birnin Shenzhen cibiyar harkokin fasaha dake kudancin kasar Sin. Kuma a cewar mashirya taron, za a gudanar da shi ne ta kafar bidiyo da kuma ido da ido.

Yayin taron manema labarai da mashirya baje kolin suka kira, an bayyana cewa, za a baje dumbin hajoji a wuri mai fadin sakwayamita sama da 140,000.

Baje kolin na bana mai taken "Sauya alkiblar makoma ta hanyar fasaha, da samar da ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire,", mashiryansa sun ce zai samu masu baje hajoji daga cikin gida da kasashen waje sama da 3,300. Kuma ana sa ran baje shirye-shirye kusan 10,000 a kuma gudanar da ayyuka 140.

Da yake tsokaci game da bikin, mataimakin magajin garin Shenzhen Ai Xuefeng, ya ce manufar baje kolin ita ce yayata hade sassan ci gaba, da bunkasa masana'antu, kimiyya da fasaha, da fannin hada hadar kudi, kuma bikin zai taka rawar gani a fannin raya kimiyya da fasaha, da kere kere, da habaka tattalin arziki. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China