Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya gabatar da muhimmin jawabi a taron kolin SCO
2020-11-10 19:57:36        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron kolin majalisar shugabannin kasashe na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai karo na 20 da aka bude da yammacin yau a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin tare da gabatar da muhimmin jawabi.

A jawabin nasa, Xi ya bayyana cewa, daukacin bil-Adam na zaune cikin kauye guda, kuma muradu da makomar dukkan kasashe a hade suke. Al'ummomin kasashen duniya suna son rayuwa mai kyau, kana babu wanda zai canja tsarin da ake ci yanzu na neman zaman lafiya da ci gaba da yin hadin gwiwa da samun moriya tare.

A bisa halin da ake ciki, wajibi ne kungiyar SCO ta kara sadaukar da kai da yin hadin gwiwa da kara ba da gudummawa ga tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasashen dake shiyyar.

Ya ce kasar Sin, ta gabatar da shawarwari ga mambobin kasashen CDC, da su kafa wani layi na kwarta kwana, kuma kasar a shirye take ta duba bukatun kungiyar a fannin riga kafi.

Xi, ya ce "wajibi ne mu goyi bayan kasashen da abin ya shafa, wajen ciyar da ajandar siyasar kasashen gaba kamar yadda doka ta tsara, da goyon bayan kasashe wajen tabbatar da tsaro da inganta rayuwar jama'a, da nuna adawa ga tsoma bakin kasashen waje cikin harkokin cikin gidan kasashe mambobin kungiyar ta kowace fuska."

Shugaba Xi ya kara da cewa, ci gaba cikin hadin gwiwa shi ne ci gaba na hakika, kana ci gaba mai dorewa, shi ne ci gaba mai kyau. A don haka, wajibi ne mu kara yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, don taimakawa farfadowar tattalin arziki da inganta rayuwar jama'a.

Ya kara da cewa, bambancin tsakanin wayewar kai mai da maras kyau kawai, shi ne abubuwan da suka kunsa. Ya ce, yana da muhimmanci a yayata akidar koyi da juna, da koyi da wayewar kan juna da yayata makwabtakar abokantaka mai kyau tsakanin dukkan kasashe.

Haka kuma, wajibi ne mu aiwatar da tsarin cudanya tsakanin bangarori daban-daban, da inganta tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa, da martaba odar duniya a kuma gani a aikace. Ya zama wajibi mu martaba akidar tuntubar juna, da ba da gudummawa da raba nasara tare, kana mu san cewa, ya kamata dukkan kasashe su rika sassantawa kan harkokin kasa da kasa

Xi Jinping, ya sake jaddada cewa, kasar Sin ita kadai ba za ta samu ci gaba ba idan babu goyon bayan sauran kasashen duniya, kamar sauran kasashe suke bukatar kasar Sin. Kasar Sin za ta nace ga tsarin samun nasara tare, da neman bunkasuwa, ta yadda ci gaban kasar Sin zai amfani duniya baki daya. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China