Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar bude taron dandalin kasa da kasa na tattaunawar kimiyya da kirkire kirkire na dandalin Boao
2020-11-10 11:34:10        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, a ranar Talata ya aike da sakon taya murnar bude taron kasa da kasa karo na farko na tattaunawar kimiyya da kirkire kirkire karkashin dandalin tattaunawar harkokin Asiya na Boao.

Xi ya bayyana cewa, sabon zamani na juyin juya halin cigaban kimiyya da fasaha da sauye sauye a fannin masana'antu sun samar da sabbin hanyoyin warware kalubalolin cigaban kasa da kasa da sauran kalubalolin duniya.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata dukkan bil adama su amfana daga cigaban kimiyya da fasaha. A halin yanzu, duniya tana fuskantar tarin kalubaloli masu yawa kamar annobar cutar numfashi ta COVID-19. Kasar Sin a shirye take tayi aiki tare da sauran kasashen duniya domin bunkasa cigaban kimiyya da fasahar kirkire kirkire da yin hadin gwiwa, da kara bude kofarta, da yin mu'amalar cin moriyar juna a tsakanin kasa da kasa a fannonin kimiyya da fasahar kirkire kirkire, don bayar da gudunmawa ga farfadowar tattalin arzikin duniya da lafiyar jama'a. ya kara da cewa, yadda dandalin Boao na tattaunawar harkokin Asiya, da gwamnatin yankin musamman ta Macao, suka yi hadin gwiwa domin karbar bakuncin taron na kasa da kasa na bunkasa cigaban kimiyya da fasahar kirkire kirkire, zai samar da muhimmin dandalin musaya da hadin gwiwa a fannin bunkasa cigaban kimiyya da fasahar kirkire kirkire a duniya.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China