Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'ar Johns Hopkins: Yawan Amurkawa da suka kamu da COVID-19 ya zarce miliyan 10
2020-11-10 11:15:51        cri

Jimillar adadin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar Amurka yayi matukar muni inda adadin ya kai miliyan 10 ya zuwa ranar Litinin, kamar yadda cibiyar bunkasa kimiyya ta CSSE dake jami'ar Johns Hopkins ta Amurkar ta sanar.

A bisa ga alkaluman hukumar CSSE, adadin mutanen da suka harbu da annobar COVID-19 a kasar Amurka ya kai 10,018,278, yayin da mutane 237,742 cutar ta yi ajalinsu, ya zuwa karfe 1:25 na tsakar ranar Litinin, daidai da karfe 18:25 agogon GMT.

Kawo yanzu, Amurka ce kasar da annobar tafi yi wa mummunar illa, kana ita ce kasar da tafi yawan mutanen da suka mutu a sanadiyyar annobar a duk fadin duniya, inda kawo yanzu kasar ke da kusan kashi 20 bisa 100 na yawan mutanen da suka kamu da kuma mutanen da cutar ta hallaka a duk duniya.

Yawan mutanen da cutar COVID-19 ta kama a Amurka miliyan 5 ne ya zuwa ranar 9 ga watan Ogasta, amma adadin ya ninka a cikin watanni uku kacal.

A makon jiya, Amurkar tana cigaba da fuskantar karuwar masu kamuwa da cutar a kullum.

Haka zalika, a cewar jami'ar ta Johns Hopkins, a kowace rana ana samun yawan mutanen da suka kamu da cutar kimanin 100,000 a cikin kwanaki biyar a jere ya zuwa ranar 8 ga watan Nuwamba.

Bisa ga irin halin ake ciki yanzu, hukumar lafiya da bincike ta kasar dake jami'ar Washington ta yi hasashen yiwuwar mutuwar mutane 399,163 a sanadiyyar cutar ta COVID-19 a Amurka ya zuwa ranar 1 ga watan Fabrairun shekarar 2021.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China