Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CIIE, wata dama ta raya tattalin arzikin duniya
2020-11-11 15:38:55        cri

A ranar Laraba 4 ga watan Nuwamban shekarar 2020 ne, aka bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga ketare karo na 3 a birnin Shanghai. Sai dai duk da tasirin annobar COVID-19 dake damun wasu sassa na duniya, yawan fadin shaguna a bikin na bana, ya karu da kashi 14% bisa na bikin da ya gabata. Kana a karon farko, kimanin kamfanoni 50 cikin 500 dake kan gaba a duniya ne, suka shiga baje hajojinsu a wannan biki.

Ban da wannan kuma, gomman kamfanoni sun kulla yarjejeniyar shiga bikin a shekaru 3 masu zuwa, abin ke nuna cewa, za a baje daruruwan sabbin kayayyaki da fasaha da hidimomi a duniya a karon farko a nan kasar Sin.

A bukukuwa biyu da suka gabata, an fi mayar da hankali ne kan wasu manyan na'urori masu kwakwalwa, sai dai a wannan karo kamfanoni daban-daban sun kara gabatar da sabbin injuna a wannan fanni.

Haka kuma kamfanoni daban-daban sun baje kayayyakinsu a Shanghai, don more damammaki da zarafin bunkasuwar kasuwannin kasar Sin.

Karfin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin da alkawarin da kasar take yi na kara bude kofa ga waje, ya baiwa kamfanonin kasashen waje kwarin gwiwar habaka zuba jari a kasar da ci gaba da raya sha'anoninsu.

Bikin baje kolin na CIIE, ya nunawa duniya yadda kasar Sin ta yi nasarar dakile yaduwar annobar, da ma raya tattalin arzikinta, ta kuma taimaka wajen tabbatar da farfadowar tattalin arzikin duniya, gami da baiwa kanana da matsakaitan kamfanoni na kasashe daban daban damar raya harkokinsu.

Alkaluma sun tabbatar da cewa, kasar Sin ta yi nasarar raya tattalin arzikinta cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce, ta hanyar bude kofarta ga kasashen waje.

Wannan ya sa, jagororin kasar kara tabbatar da cewa, a nan gaba kasar za ta kara bude kofarta, don neman samun ci gaban tattalin arziki mai inganci. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China