Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CIIE: Kayayyaki Kala-kala Sun Ba Da Damar Neman Ci Gaba Tare
2020-11-09 19:02:03        cri

 

 

Ban da kayayyaki masu fasahohi na zamani, da aka gabatar a bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasuwannin kasar Sin daga ketare karo na 3 dake gudana a birnin Shanghai na kasar Sin, an kuma nuna abinci da kayayyakin da aka sarrafa da hannu na wasu kasashe masu tasowa, da wadanda ba su da karfin tattalin arziki, kayayyakin da suka hada da gahawa na kasar Angola, da darduma na kasar Iran, gami da sabulu na kasar Lenanon.

Kamfanoni na kasashe daban daban suna kallon bikin CIIE a matsayin wata kofar shiga cikin kasuwannin kasar Sin. A bukukuwan CIIE guda 2 na baya, kimanin kanana da matsakaitan kamfanoni 100 na kasashe marasa karfin tattalin arzikin fiye da 20, sun samu damar nuna kayayyakinsu.

Kana a wannan karo, kasar Sin na ci gaba da kokarin saukakawa bakin da suka zo daga wadannan kasashen, inda ake samar musu da rumfuna, da hidimar jigilar kaya, da dai sauransu kyauta. Bayanai na nuna cewa, wasu kasashe marasa karfin tattalin arziki 30 sun turo tawagogi don halartar biki na bana.

A sakamakon annobar COVID-19, yawan cinikin kasa da kasa ya sauka zuwa kasa a rubu'i na biyu na wannan shekarar da muke ciki. Lamarin da ya sanya MDD hasashen wasu mutane miliyan 71 za su iya komawa cikin yanayi na matukar talauci. A daidai wannan lokaci, kasar Sin ta yi nasarar shawo kan yanayin yaduwar cutar COVID-19, har ma ta bude bikin CIIE kamar yadda aka shirya, tare da raba damammaki na shiga cikin kasuwannin kasar, da na samun ci gaba, tare da baki na kasashe daban daban. Haka wata dama ce mai kyau ta taimakawa kasashe masu tasowa raya tattalin arzikinsu.

Hakika, abun da kasar Sin ke samarwa al'ummar duniya a wannan karo, ba babbar kasuwa kawai ba, wata dama ce ta samun ci gaba tare. Kakakin kungiyar ciniki ta duniya WTO, Keith Rockwell, ya ce bikin CIIE zai gabatar da kamfanonin kasashe marasa karfin tattalin arziki ga takwarorinsu na kasar Sin da na sauran kasashe daban daban, ta yadda za su samu damar shiga a dama da su a tsarin ciniki na duniya. Hakan ya kara tabbatar da kokarin kasar Sin na kafa al'umma mai kyakkyawar makomar bil Adama ga daukacin bil-Adama. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China