Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Farfadowar kasuwar kasar Sin ya baiwa 'yan kasuwan kasashen waje kwarin-gwiwa
2020-11-09 14:27:21        cri


Ana ci gaba da gudanar da bikin baje-kolin hajojin da ake shigowa da su kasar Sin ko kuma CIIE a takaice karo na uku a birnin Shanghai dake gabashin kasar. A yayin da annobar COVID-19 ke ci gaba da addabar duniya, kasuwar kasar Sin tana farfadowa sosai, al'amarin da ya karfafa gwiwar baki 'yan kasuwa dake halartar bikin.

"Yau muna gabatar da hajojin kamfaninmu na NUTRICIA kai-tsaye daga nan wajen bikin CIIE, kuma za mu yi muku ragi da garabasa……"

A wajen bikin CIIE a wannan karo, akwai kamfanoni da mutane da yawa wadanda suke amfani da kafar intanet domin gabatar da kayayyakinsu kai-tsaye. Shahararren kamfanin samar da kayan kwalliya ta kasar Faransa wato L'Oreal na daya daga cikinsu.

A nasa bangaren, wani jami'in kamfanin L'Oreal mai suna Chen Jiaqi ya bayyana cewa, kafin bikin, kamfaninsa ya riga ya fahimci muhimmiyar rawar da kafar intanet ke takawa a fannin tallata kaya. Musamman a lokacin da ake fama da annobar COVID-19, sayar da hajoji ta kafar intanet ya taimaka sosai ga habaka kasuwancinsu a kasar Sin.

Mista Chen Jiaqi ya ce:

"A yayin da cutar COVID-19 ke yaduwa, mun fahimci mutane suna da matukar sha'awar sayayya ta kafar intanet. Shi ya sa tun tuni muka soma tsara shirin gudanar da kasuwanci ido da ido da kuma ta kafar intanet, abun da ya sa muka iya tinkarar kalubalen cutar, da fardado da kasuwancinmu yadda ya kamata."

Bisa alkaluman kididdigar da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayar, daga watan Janairu zuwa Satumbar bana, darajar hajojin da aka sayar da su a kasuwar kasar ta zarce triliyan 27.3, kana wannan adadin ya karu da kaso 0.9 daga watan Yuli zuwa Satumba. Ke nan, kasuwar kasar Sin ta fi ta sauran kasashen duniya farfadowa cikin sauri, al'amarin da ya karfafa gwiwar kamfanonin kasashen waje don su ci gaba da zuba jari a kasar.

A nasa bangaren, babban jami'in kamfanin BSH dake samar da kayan lantarkin gida reshen kasar Sin, Mista Christof Jaeger ya ce:

"Muna cikin mawuyacin hali tun farkon shekarar da muke ciki, musamman ana samun koma-bayan tattalin arzikin duniya sosai. Amma kasar Sin ta samu babbar nasarar dakile yaduwa cutar, har ma tattalin arzikinta ya bunkasa. A sakamakon haka, daga watan Janairu zuwa Satumbar bana, cinikinmu a kasar Sin har ya zarce na makamancin lokacin bara. Mun yi hasashen cewa, cinikinmu zai karu a kasuwar kasar Sin bana. Kuma muna da yakinin cewa ci gaba ne mai dorewa."

Cutar COVID-19 ta sa al'ummar kasar Sin kara maida hankali kan batun da ya shafi lafiya. A wajen bikin CIIE a bana, ana baje-kolin wasu kayayyakin zamani daban-daban da suka shafi hikimar rayuwa, ciki har da na'urar wanke kwano, da na'urar tsabtata daki, har ma da na'urar tace iska, wadanda za su iya biyan bukatun al'umma a fannin kawar da kwayoyin cuta da samun rayuwa mai tsabta da lafiya.

Har wa yau, a lokacin da ake fama da cutar COVID-19, akwai mutane da dama wadanda suka fara maida hankali kan motsa jiki a gida don inganta lafiya, al'amarin da ya samar da damammakin kasuwanci ga kamfanonin samar da kayan motsa jiki na kasashen waje. Jami'ar dake kula da harkokin waje ta shahararren kamfanin samar da kayan motsa jiki na kasar Faransa mai suna Decathlon reshen kasar Sin, Zhu Yiling ta ce:

"Da cutar ta fara yaduwa, mun gano wasu sabbin sauye-sauyen da suka wakana game da harkokin motsa jiki na al'umma, wato sun fi son abubuwa masu saukin dauka, a sabili da haka, mun samar da irin wadannan kayayyaki, ciki har da wani nau'in na'urar gudu, wadda ake iya nadewa a saka shi karkashin gado ko a jingine a jikin bango."

A wajen bikin CIIE na bana, baki 'yan kasuwa daga kasashe daban-daban sun zo da sababbin hajojinsu da yawa, wadanda karon farko suka baje-kolinsu a kasar Sin, har ma sun samar da wasu hajoji musamman ga kasuwar kasar, inda suka bayyana cewa, suna da yakinin cewa kasuwar kasar Sin za ta samu kyakkyawar makoma kuma za su kara zuba wa kasar jari.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China