Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta tura tawagar jami'an lafiya don taimakawa yaki da COVID-19 a Gambia
2020-11-08 19:57:40        cri
A yau Lahadi wata tawagar ayarin jami'an kiwon lafiya ta kasar Sin ta tashi daga birnin Shenyang, helkwatar lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar, zuwa kasar Gambia inda za su shafe tsawon watanni uku don gudanar da ayyukan tallafin kiwon lafiya ga kasar ta yammacin Afrika wajen yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Tawagar ta kunshi kwararrun masana kiwon lafiya 9 daga lardin, wadanda suka kware a fannin kula da masu fama da tsananin jinya, da masana cutuka masu yaduwa, da kuma kwararru a fannin matsalar sarkewar numfashi.

Haka zalika, akwai kuma wata tawagar ta daban ta kwararrun likitoci 10 da suka tashi daga birnin na Shenyang zuwa kasar Gambia duk a wannan rana inda za su gudanar da aikinsu na tsawon shekara guda. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China