Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNICEF ya bayyana damuwa game karuwar hare-hare kan makarantu a Kamaru
2020-11-07 17:07:24        cri

Asusun kula da yara ta MDD UNICEF, ya bayyana damuwa game da karuwar hare-hare kan makarantu da cibiyoyin ilimi a yankunan arewa masu yammaci da kudu maso yammacin Kamaru.

A cewar asusun, tun bayan komawa makaranta a bana, cikin kasa da wata guda da ya gabata, an samu rahotanni da dama na sace-sace da cin zarafi da kashe kashen da suka shafi dalibai da malamai.

Daraktar asusun a yankunan yammaci da tsakiyar Afrika, Marie-Pierre Poirier, ta bayyana hare-haren a matsayin wadanda ba za a amince da su ba, tana mai cewa makarantu wurare ne na koyon ilimi, inda kuma ya kamata yara su kasance cikin aminci da tsaro. Ta yi kira ga dukkanin bangarorin kasar, su tabbatar da ba dukkan yara kariya a makarantu ko cikin unguwanni, sannan su daukaka ka'idar yarjejeniyar tabbatar da tsaro a makarantu, wadda ke kira da dakatar da kai hare-hare kan makarantu da cibiyoyin ilimi da jami'ansu.

Asusun ya ce, cikin shekarar 2019, an kai hare-hare kan makarantu har sau 35 a yankunan na Kamaru masu fama da rikici. A bana kuwa, an samu hare-hare 17 kawo yanzu, inda ake alakanta raguwar adadin da rufe makarantun da aka yi tsakanin watan Maris da Yuni, sakamakon bullar annobar COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China