Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi taro karo na 9 na dandalin tattaunawa tsakanin masanan Sin da Afirka
2020-11-06 10:59:53        cri

Jiya Alhamis, an yi taro karo na 9 na dandalin tattaunawa tsakanin masanan Sin da Afirka a Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Taron mai taken "Cikar shekaru 20 da kafa dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar Sin da Afirka: Yin waiwaye adon tafiya da hango makoma", ya samu halartar kwararru da masana da jami'an gwamnati da dama daga bangarorin biyu, ciki har da mai taimakawa ministan harkokin wajen Sin Deng Li, da tsohon shugaban kasar Mozambique Joaquim Alberto Chissano, da jakadun wasu kasashen Afirka dake kasar Sin da sauransu.

Dandalin tattaunawa tsakanin kwararrun Sin da Afirka, wani muhimmin sashi ne na dandalin tattaunawar hadin-gwiwar Sin da Afirka wanda aka fi sani da FOCAC a takaice, wanda aka kafa shi tun a shekara ta 2011. An kafa dandalin ne da nufin sa kaimi ga nazarin batutuwan da suka shafi Sin da Afirka, da kara fahimtar juna da fadada cimma matsaya tsakaninsu, a wani kokari na ingiza bunkasar huldar Sin da Afirka.

A jawabin da ya gabatar, mai taimakawa ministan harkokin wajen Sin Mista Deng Li ya ce, a halin yanzu tattalin arzikin duniya na fuskantar koma-baya da kalubaloli da dama, har ma wasu kasashe na ci gaba da nuna babakere da ra'ayi na kashin kai a harkokin kasa da kasa, amma duk da haka, hadin-gwiwa da mu'amalar da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka na ci gaba da bunkasa.

Ya ce, bayan da aka kafa irin wannan dandalin tattaunawa, wato na masana da kwararrun Sin da Afirka, masana daga bangarorin biyu suna ta bada muhimman shawarwari game da yadda za a raya huldodin Sin da Afirka. Mista Deng ya bayyana fatansa ga masana da kwararrun Sin da Afirka, inda ya ce: "Ina fatan masana da kwararrun Sin da Afirka za su shiga cikin al'umma, da yin tattaki zuwa wuraren da ake gudanar da ayyukan hadin-gwiwa tsakanin bangarorin biyu, domin samar da goyon-baya ga raya ci gaban dangantakarsu. Ina kuma fatan za su bullo da wasu kwararan matakai, musamman a fannonin da suka shafi gina yankin gudanar da kasuwanci maras shinge, da kiwon lafiya, da fasahar sadarwar 5G da sauransu."

Sa'an nan a nasa bangaren, tsohon shugaban kasar Mozambique Joaquim Alberto Chissano ya gabatar da jawabin cewa, dadadden zumunci da hadin-gwiwar Sin da Afirka ya kai wani sabon matsayi yanzu, kuma wannan dandalin tattaunawar da aka kafa tsakanin kwararru da masanan Sin da Afirka, zai kara taimakawa ci gaban kyakkyawar dangantakar bangarorin biyu. Mista Chissano ya ce: "Bana ta cika shekaru 20 ke nan da kafa dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, inda muke farin-cikin ganin nasarorin da aka samu, yayin da kuma muke kokarin kara kyautata zaman rayuwar al'ummominmu baki daya. A halin yanzu, duniyarmu tana fuskantar yanayi na rashin tabbas da kalubaloli daban-daban, musamman yaduwar annobar COVID-19, abun da ya haifar da babbar barazana ga al'ummun duniya baki daya, musamman tsananta matsalar talauci da wasu kasashen Afirka suke fama da ita. Tsarin FOCAC gami da shawarar ziri daya da hanya daya, babu tantama za su taimaka sosai ga hada kan bangarori daban-daban, wajen shawo kan wadannan kalubaloli da kuma farfado da zaman rayuwa gami da tattalin arzikin duniya."

Shi ma Mista Cai Fang, mataimakin shugaban cibiyar nazarin zaman rayuwar al'umma ta kasar Sin, kana shugaban cibiyar nazarin batutuwan Afirka ta kasar Sin, ya ce, shekarar da muke ciki, shekara ce da kasar Sin take fatan cimma muradunta na raya al'umma mai matsakaiciyar wadata. Rage fatara, buri ne da daukacin al'umma suke kokarin neman cimmawa. Kasar Sin tana fatan fadada hadin-gwiwa da mu'amala da kasashen Afirka musamman a fannin kawar da talauci da neman ci gaba.

Mista Cai ya kara da cewa: "A watan Oktoban bana, kwamitin tsakiya karo na 19 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya kira cikakken zamansa na 5, inda aka bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da fadada bude kofarta ga kasashen waje, da inganta shawarar 'ziri daya da hanya daya', da shiga ayyukan yin kwaskwarima ga tsarin tattalin azikin duniya. Sin na fatan himmatuwa tare da kasashen Afirka, domin ci gaba da gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya." (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China