Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kayan Aro ba ya Rufe Katara
2020-11-04 19:15:13        cri

Duk wata kasa da ta amsa sunanta, wajibi ne ta dogara da kanta a fannoni daban-daban, idan tana son tsare kima da darajarta. Wannan ne ya sa, kasashe ke tsara manufofi da shirye-shiryen raya kasa, walau na dogo ko gajeren lokaci, domin kare mutuncinsu da na jama'arsu daga dukkan fannoni.

Ita ma kasar Sin, kamar sauran kasashe ba a bar ta a baya ba, wajen fito da irin wadannan shirye-shirye na raya tattalin arziki da jin dadin al'ummar Sinawa na tsawon shekaru biyar-biyar, da ma na dogon zango da take fatan cimmawa zuwa wani wa'adin shekaru.

A shekarar 2020 da muke ciki ne, kasar ta kammala aiwatar da shirin raya kasa da ta tsara daga shekarar 2016-2020. Yanzu haka an gabatar da shawarwari game da shirin raya kasar na shekarar 2021-2026 da ma na dogon zango zuwa shekarar 2035 da ake fatan cimmawa.

Sai dai, wai hanzari ba gudu ba, kwamitin koli na JKS dake fasalta shirin raya tattalin arzikin da rayuwar al'ummar Sinawa na shekaru biyar karo na 14, da manufofi na dogon zango da ake fatan cimmawa nan da shekarar 2035, ya sanar da cewa, kirkire-kirkire shi ne jigon shirin zamanantar da kasar Sin.

Masu fashin baki na cewa, idan har kasar Sin tana son cimma wannan buri, wajibi ne ta dogara da kanta a fannin kimiya da fasaha, ta yadda za ta tunkari ci gaban kimiya da fasaha na duniya, da matsalar tattalin arziki, da manyan bukatun kasa da batun da ya shafi kiwon lafiya da rayuwar al'umma, da kara aiwatar da matakan farfado da kasa ta hanyar kimiya da ilimi, da kara karfin kasa ta hanyar amfani da masana da bunkasa kirkire-kirkire, da inganta tsarin kirkire-kirkire, ta yadda za a kara karfin kimiya da fasahar kasar.

Daga cikin manyan ayyuka 12 da aka gabatar wajen tsara shirin, shi ne, nacewa ga raya kirkire-kirkire, a kuma dunkule sabbin nasarorin da aka cimma.

Idan har aka karfafa dabarun raya kasa a fannin kimiya da fasaha, da kara karfin kamfanoni a fannin kirkire-kirkire, da karfafa gwiwar masu basirar kirkire-kirkire da inganta tsari da matakan kirkire-kirkire na kimiya da fasaha, babu tantata kasar Sin za ta cimma burinta na zama kasa mai dogaro da kanta a fannin kimiya da fasahar kere-kere da ma sauran fannoni. Guntun Gatarinka, aka ce ya fi Sari ka ba ni. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China