2020-11-04 14:18:54 cri |
A daren ranar 4 ga watan da muke ciki, za a bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasar Sin (CIIE) karo na 3, a birnin Shanghai dake gabashin kasar. Inda "tsofaffin abokai" da suka zo kamar yadda aka alkawarta, ko kuma "sabbin abokai" da suka zo wajen bikin a karon farko, dukkansu suna fatan yin amfani da wannan dandalin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa don raba ribar kasuwar kasar Sin da raba damammakin kasuwancin duniya.
Ko da yake bikin CIIE na wannan karo za a gudanar da shi ne a yayin da ake tinkarar yaduwar annobar COVID-19, amma kamfanoni daga kasashe daban-daban suna sa himman wajen halartar bikin. Jimillar fadin yankin baje kolin wannan CIIE ya fadada da kusan murabba'in mita 30,000 idan aka kwatanta da na baya. Kamfanoni 500 da suka fifice a duniya da manyan kamfanoni a sana'o'i daban daban sun bayyana fatansu sosai na shiga bikin, har ma adadin dawowarsu ya wuce 70%.
Shugaban hukumar darektocin kamfanin harhada gilasan magunguna na duniya dake kasar Jamus SCHOTT, Frank Heinricht ya bayyana cewa ya halarci CIIEs har sau uku., kuma kamfaninsa ba zai taba kauracewa bikin CIIE ba, saboda raba damammakin kasuwanci tare. Idan aka kwatanta da na baya, kamfanin SCHOTT ya kara fadin yankin rumfarsa da kashi 50%, kuma abubuwan da ya baje kolinsu suna da yawa.
"A cikin shekaru biyu da suka gabata, dandalin CIIE da gwamnatin kasar Sin ta gina ya burge mu kwarai da gaske. Muna yaba da kyawawan matakan da hukumomi da ma'aikatan da abin ya shafa suka dauka, don ba da tabbaci ga shirya bikin na bana a lokacin da aka tsaida. Kasar Sin ita ce kasuwar bunkasar mu ta farko, ba kawai muna kokarin zuba jari ne a kasar Sin ba, har ma muna shirin kara saurin tafiyarmu don karfafa kulla kawance da kasar Sin."
Kasar Sin tana kan gaba wajen shawo kan annobar COVID-19 da kuma shiga matakan farfado da tattalin arziki cikin sauri a duniya, hakan ya sa kamfanoni masu jarin waje cike da kwarin gwiwa game da makomar kasuwar kasar, kamfanonin kasashen ketare masu yawa da suka shiga bikin baje kolin, sun sanya hannu kan "kwangilar dogon lokaci" don shiga bikin CIIE na shekaru 3 masu zuwa, ciki har da kamfanin SHISEIDO na kasar Japan. A cikin rubu'i na biyu na wannan shekarar, sha'anin SHISEIDO a kasar Sin ya cimma nasarar farfadowa, wanda ya kasance irinsa na farko a cikin harkokin kamfanin. Hase Naoko, daraktar gudanarwa ta kamfanin dake kasar Sin, ta ce kamfaninta, na fatan yin amfani da dandalin CIIE don kara saka jari a kasar Sin.
"A kasuwar kasar Sin, mun gina wata kyakkyawar makoma. Bisa yanayin da muke ciki na yaki da annobar COVID-19, kasar Sin ce kadai ta samu saurin farfadowar tattalin arziki, don haka muna da tsare-tsaren saka jari masu dacewa a fannoni daban daban a kasar Sin. A bikin na wannan karo, mun ninka fadin rumfa har sau biyu bisa na bara. Saboda a lokacin da muka halarci CIIE na baya, mun ji babban tasirin wannan dandamali da kuma muhimmancinsa, don haka muka kara fadin yankin baje kolinmu, da nufin gabatar da sabbin bayananmu da kuma yada sabbin kayayyakinmu ta hanyar CIIE."
Kamfanin LOREAL na kasar Faransa, shi ma ya amfana da daidaiton kasuwar masarufin kasar Sin. A cikin watanni shida na farkon shekarar da muke ciki, sakamakon yaduwar annoba, cinikin kamfanin a sassa daban daban na duniya ya yi kasa, amma harkar kamfanin a babbar kasuwar kasar Sin ta yi rawar gani, inda cinikayyar ta karu da kaso 20.8 a cikin rubu'i na uku na bana. Kyakkyawan yanayin kasuwar kasar Sin ya sa harkokin kamfanin a duniya ya ci gaba yadda ya kamata a cikin rubu'i na uku. A bana, kamfanin mai jarin waje dake cin gajiyar kasuwannin kasar Sin ba kawai ya kawo sabbin kayayyaki biyar ne zuwa bikin CIIE ba, har ma ya dauki CIIE a matsayin wata kafa ta nuna sabbin kayayyaki da fasahohi masu yawa. Shugaban kamfanin, kuma daraktan zartaswa na kamfanin Jean-PaulAgon ya ce,
"Yadda aka shirya bikin CIIE a lokacin da aka tsara, ya aike wa duniya wata alama cewa, kasar Sin ta farfado daga yaduwar annobar COVID-19, wanda kuma ya nuna aniyar kasar ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta bunkasuwar duniya bisa ra'ayinta na bude kofa da cimma nasara tare. Mun yi imanin cewa, a kasar Sin mai salon bude kofa, da hadin kai, da kirkire-kirkire, da dorewa kuma mai daukar nauyinta, tana maraba da kowa, don raba kyakkyawar makoma da duniya baki daya. Babu abin da zai girgiza imaninmu."
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China