Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babbar Canzawar Da Aka Samu Kan Wata Tsohuwar Ma'aikata
2020-11-06 08:13:04        cri

 

 

Wani wurin shakatawa mai suna "27 Park", ya shahara sosai a birnin Beijing na kasar Sin. Saboda an samu wannan wuri ne ta hanyar yin kwaskwarima kan wasu tsoffin gine-ginen wata tsohuwar ma'aikatar sarrafa kan jirgin kasa.

 

Wannan ma'aikata tana da tarihi sosai, sai dai zuwa wannan zamani da muke ciki, fasahar ma'aikatar ta zama tsohon yayi, saboda haka gwamnatin birnin Beijing, da masu kula da ma'aikatar suka yanke shawarar dakatar da ayyukan wannan ma'aikata, sa'an nan aka yi amfani da filaye da gine-ginenta, don kafa wata cibiyar horaswa ta fasahohin wasannin da ake yi a kan kankara, gami da wani wurin shakatawa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China