Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Pakistan ta sha alwashin yakar ta'addanci
2020-11-04 12:11:59        cri
A baya bayan nan, ana samun yawaitar haren ta'addanci da ake kaiwa kasar Pakistan. Galibin hare-haren ana kaiwa ne kan jami'an tsaro da makarantun addini. Gwamnatin Pakistan da shugabannin sojojin kasar sun bayyyana cewa za su ci gaba da daukar matakan kawar da ayyukan ta'addancin. Hukumomin tattara bayanan sirri da bangarorin shari'ar kasarsu ma suna daukar kwararan matakan yakar ayyukan ta'addanci a kasar.

Sojojin Pakistan sun sanar a ranar 15 ga watan Oktoba cewa, lardin Balochistan dake kudu maso yammacin kasar da yankin North Wazirista dake shiyyar arewa maso yammacin kasar sun kasance wasu yankuna biyu dake yawan fama da hare-haren ta'addanci da ake kaiwa kan sojojin kasar ta Pakistan, a kalla an kashe mutane 20. A ranar 27 ga watan Oktoba, an kashe wasu dalibai 8 sannan kimanin mutane 120 ne suka samu raunuka a harin bam da aka kaddamar kan wasu makarantun addini a birnin Peshawar dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Bayan hare-haren da aka kaddamar kan makarantun addinin a birnin na Peshawar, firaministan kasar Imran Khan, ya bayyana a kafafen sada zumunta cewa, ya bada tabbacin binciko dukkan 'yan ta'addan domin hukunta su nan ba da jimawa ba. Shi ma babban hafsan sojojin kasar ta Pakistan Qamar Javed Bajwa, ya fada a lokacin da ya ziyarci mutanen da suka samu raunuka a sanadiyyar harin, ya tabbatar da cewa, sojojin Pakistan za su murkushe 'yan ta'addan da masu taimaka musu.

A martani da ta mayar game da karuwar hare-haren ta'addanci a kasar, hukumar yaki da ayyukan ta'addanci ta kasar Pakistan ta fitar da bayanan gargadi game da hare-haren na watan Oktoba, inda take tunatar da jama'a su zauna cikin shirin ko ta kwana wajen daukar matakan tsaro don samun kariya a lokacin da ake gudanar da tarukan siyasa da na addini a kasar. A hannu guda kuma, jami'an tsaron kasar Pakistin da 'yan sanda suna ci gaba da daukar kwararan matakan yaki da ayyukan ta'addanci da kuma a yankunan dake fama da rikice-rikicen kabilanci a lardin Balochistan dake makwabtaka da kasar Afghanistan. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China