Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta tsara ginshikan ci gabanta na shekaru 5 masu zuwa
2020-11-03 20:55:40        cri

Kasar Sin ta sha alwashin cimma nasarar bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'ummarta cikin shekaru 5 dake tafe, kamar dai yadda hakan ke kunshe, cikin kundin bayanai da kwamitin tsara shawarwarin samar da ci gaba na JKS ya fitar a Talatar nan.

Kundin shawarwarin ya nuna kudurin Sin, na kara azama wajen bunkasa tattalin arzikin kasa. Inda karkashin hakan, za a aiwatar da matakai daban daban na gudanar da sauye sauye da bude kofa, kuma kasar za ta zurfafa salon gurguzu a fannin raya kasuwanni, tare da kammala gina tsarin kasuwa mafi inganci.

Har ila yau, kundin ya nuna yadda Sin ke fatan kara kyautata dabi'u da tsarin rayuwar al'ummun ta, yayin da al'ummar kasar ke dada rungumar salon zurguzu na hakika.

Kundin ya fayyace cewa, babban burin Sin shi ne, sabunta samun ci gaba mai kunshe da dabarun kyautata muhallin halittu, da kara inganta rayuwar jama'a, da fadada ikon hukumomi na sauke nauyin dake wuyan su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China