Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alassane Ouattara ya lashe zaben Cote d'Ivoire
2020-11-03 19:37:10        cri

Alkaluman sakamakon zabe da hukumar zaben kasar Cote d'Ivoire ta fitar sun nuna cewa, shugaban kasar mai ci Alassane Ouattara, ya lashe babban zaben da aka kada a ranar Asabar din karshen makon jiya, bayan da ya samu kaso sama da 94 bisa dari na daukacin kuri'un da aka kada.

A cewar hukumar zaben kasar, Ouattara ya samu kuri'u 3,031,483, don haka ya yi nasarar sake komawa kujerar shugabancin kasar.

Cikin jimillar kuri'u 6,066,441 da aka kada, hukumar zaben kasar ta tace kuri'u 3,269,813 masu inganci, wadanda aka kada a rumfunan zabe 17,601 dake sassan kasar, adadin da ya yi daidai da kaso 53.90 bisa dari na masu kada kuri'un da aka yiwa rajista.

'Yan takarar jam'iyyun adawa Henri Konan Bedie, da Pascal Affi N'Guessan, wadanda suka bukaci al'ummun kasar su kauracewa kada kuri'u, sun samu kaso 1.66 da 0.99 bisa dari, a sakamakon zaben da aka fitar yau Talata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China